Lahadi 2 Agusta 2026 - 12:27
Gwagwarmaya da Jajircewa a Gaban Maƙiyi na Daga Cikin Fitattun Darussan Rayuwar Imam Husaini (A.S) / Muhimmancin Sanin Yazidun Wannan Zamanin (Ƙarshe)

Hauza/ Saƙon gwagwarmayar Imam Husaini (A.S.) ga mutanen Iran (da ma duniya) shi ne cewa rayuwa ba ta da ƙima idan mutum zai rayu cikin wulakanci. Rayuwa ta hakika tana samun ma'ana ne cikin 'yanci, ɗaukaka da bautar Allah Maɗaukakin Sarki.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza | Wannan shi ne sashe na ƙarshe na wannan hira da Hujjatul Islam Wal Muslimin Malakzade a kan gwagwarmaya da wajibcin sanin Yazidun wannan zamanin. Duk da dai hirar ta maida hankali ne ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran, amma idan muka kalli sakon da ke ciki da kyau zamu ga cewa darussan da ke ciki sun haɗa dukkan yan gwagwarmaya musamman na addini.

Neman 'Yancin Kai da Ƙin amincewa da mamayar baƙi na daga cikin saƙonnin Ashura

Hujjatul Islam wal Muslimin Malakzade ya bayyana cewa neman 'yancin kai da ƙin amincewa da mulkin baƙi na daga cikin muhimman saƙonnin Ashura. Ya ce: "Imam Husaini (A.S.) bai yarda ya yi mubaya'a ga mutum kamar Yazid ba, wanda bai cancanci jagorancin al'ummar Musulmi ba, kuma bai amince ya miƙa wuya ga mulkinsa ba."

Ya ƙara da cewa wannan darasi yana da matuƙar muhimmanci ga al'ummar Iran ma, domin 'yancin kai yana nufin tsayawa a gaban danniya, ƙin karɓar tilastawar ƙasashen waje, da kuma ƙin miƙa makomar ƙasa ga manyan ƙasashe. Ya ce wannan ruhin neman 'yancin kai da ƙin mamaya ne ya sa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kasance, a idon al'ummomi da dama, ƙasa mai cin gashin kanta kuma mai tsayawa a gaban mamayar baƙi.

Haɗin kai a ƙarƙashin gaskiya da Wilayatul Faƙih; mabuɗin nasara a gaban maƙiyi

Ya yi nuni da cewa ɗaya daga cikin manyan saƙonnin Ashura shi ne haɗin kai da haɗuwar al'umma. Ya ce: "A Karbala mutane daga shekaru daban-daban, ƙabilu daban-daban da asali daban-daban sun kasance tare da Imam Husaini (A.S.); daga tsoho kamar Habib bn Muzahir, zuwa matashi kamar Ali Akbar (A.S.), jariri kamar Ali Asghar (A.S.), har ma da baƙar fata bawa mai suna Jun, duk sun taru ne a ƙarƙashin tutar gaskiya domin kare hakika."

Hujjatul Islam Malakzade ya ce saƙon wannan lamari ga al'ummar Iran shi ne kiyaye haɗin kai a gaban maƙiyi guda. Ya jaddada cewa nasarar tsayin daka tana samuwa ne idan dukkan sassan al'umma suka haɗu wajen fuskantar maƙiyi tare da kiyaye haɗin kansu a ƙarƙashin gaskiya da Wilayatul Faƙih.

Gwagwarmayar Imam Husaini ba ta tare da yanke ƙauna

Ya bayyana cewa fata ga makoma da kuma tabbacin nasarar gaskiya a kan ƙarya na daga cikin saƙonnin Ashura masu dawwama. Ya ce: "Gwagwarmaya a tafarkin Imam Husaini (A.S.) bai taɓa kasancewa tare da yanke ƙauna ba. Imam Husaini (A.S.) ya ci gaba da aiwatar da nauyin da Allah Ya ɗora masa har zuwa numfashinsa na ƙarshe, sannan ya bar sakamako ga Allah."

Ya ƙara da cewa wannan saƙo yana ba al'ummar Iran fata, domin bisa ga alƙawarin Allah, idan mutane suka yi haƙuri suka tsaya kan gaskiya, a ƙarshe gaskiya za ta yi nasara a kan ƙarya.

Ya ce irin wannan fahimta tana ƙarfafa al'umma a gaban matsin lambar ƙasashen waje, barazana da yaƙin tunani, kuma ba ta barin matsin siyasa, tattalin arziki, soja ko yaɗa labarai su karya fatan jama'a da ƙudurinsu.

Rayuwa ta hakika tana cikin ɗaukaka, 'yanci da bautar Allah

Hujjatul Islam wal Muslimin Malakzade ya ce: "Saƙon gwagwarmayar Imam Husaini (A.S.) ga mutanen Iran (da ma duniya) shi ne cewa rayuwa ba ta da ƙima idan mutum zai rayu cikin wulakanci. Rayuwa ta hakika tana samun ma'ana ne cikin 'yanci, ɗaukaka da bautar Allah Maɗaukakin Sarki."

Ya ci gaba da cewa makarantar Ashura tana koya wa al'ummar Iran su kafa tushensu a kan gaskiya da hakika, kada su ji tsoron barazanar maƙiyi, kuma su ci gaba da kasancewa masu tsayin daka.

Kammalawa

A ƙarshen tattaunawar tasa, Hujjatul Islam wal Muslimin Malakzade ya ce: "Al'ummomin da suke sanin maƙiyansu da basira, suke kiyaye 'yancinsu, suke haɗuwa a ƙarƙashin gaskiya, kuma suke tafiya da bege da dogaro ga Allah, ba za su yi nasara a kansu ba duk da matsin lamba da makircin maƙiya. Domin babban darasin Ashura shi ne tsayuwa cikin ɗaukaka har zuwa lokacin da gaskiya za ta yi cikakkiyar nasara."

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha